Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ce a shirye take ta taimaka wa Jamhuriyar Benin da sojoji domin daƙile juyin mulkin da wasu sojoji suka yi iƙirarin yi.
Matakin na Ecowas na zuwa ne bayan wani rukunin soji sun sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon a kafar talabijin ɗin ƙasar a ranar Lahadi tare da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta ɗora wa sojojin alhakin “duk wani rai da aka rasa” sakamakon yunƙurin nasu.

“Ecowas za ta taimaka wa gwamnati da al’umma da duk abin da ya kamata, ciki har da aika dakarun ko ta kwana domin kare tsarin mulki da kuma ‘yancin Benin,” a cewar sanarwar da hukumar Ecowas mai hedikwata a Abuja ta fitar
Sai dai hukumomi a ƙasar sun ce sun shawo kan lamurra bayan yunƙurin juyin mulkin.
“An shawo kan lamarin sannan mafi yawan rundunar soja na goya wa shugaban ƙasa baya haja kuma muna ƙara shawo kan al’amuran.” kamar yadda Ministan harkokin waje Shegun Adjadi Bakari ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters.


