Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya Afrika
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu Kiwon Lafiya
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin Afrika

Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19
Published: August 11, 2026 at 9:03 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da naɗin Manyan Sakatarori guda 19 don cike guraben aiki da ake da su a Ma’aikatun Gwamnatin Jihar da kuma ƙarfafa harkokin gudanarwa don samar da ayyuka masu inganci ga jama’a.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jiha, Farfesa Mu’azu Shehu, wanda ya sanar da amincewar Gwamnan, yace naɗin ya zama dole sakamakon rashin manyan Sakatarorin a ma’aikatu da dama, duba da ƙirƙira da sake fasalin wassu ma’aikatu da gwamnatin jihar ta yi kwanan nan.

Ya bayyana cewa cike guraben da aka rasa zai tabbatar da cewa ma’aikatun da abin ya shafa sun samu jagoranci mai inganci kuma sun samu kyakkyawan yanayin aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata.

Farfesa Shehu yace an zaɓo jami’an da aka naɗan ne don daga ƙananan hukumomi 11, tare da la’akari da yankunansu daban-daban, da ƙwarewar aiki da kuma muhimman buƙatun ma’aikatun daban-daban.

Ya jaddada cewa naɗe-naɗen an yi su ne bisa dogara da dacewa, ƙwarewa da kuma bayanan da aka tabbatar na jami’an, yana mai cewa jami’an da aka naɗan sun gudanar da kyawawan ayyuka a duk tsawon ayyukansu kuma suna da kyakkyawan tarihin aikinsu mai tsabta.

A cewarsa, an tantance jami’an sosai kuma an ga sun dace da riƙon muƙaman, bayan sun samu gogewar data dace da kuma nuna jajircewa, ƙwarewa da azama a fannoni daban-daban na ayyukansu.

Ya ƙara da cewa ƙimar aikinsu mai gamsarwa da kuma tarihin aikinsu mai tsabta sune tushe mai ƙarfi na ɗaukaka su zuwa manyan sakatarorin.

Sabbin Manyan Sakatarorin da aka naɗa su ne:

Haruna Mohammed Danburam – daga Ƙaramar Hukumar Akko

Mohammed Auwal Ahmed – daga Ƙaramar Hukumar Akko

Alheri Yoriyo – daga Ƙaramar Hukumar Balanga

Haruna Bello Gelengu – daga Ƙaramar Hukumar Balanga

Ruth Caleb Maina – daga Ƙaramar Hukumar Billiri

Auwal Abduljalal – daga Ƙaramar Hukumar Dukku

Kasimu Umar – daga Ƙaramar Hukumar Dukku

Musa Muhammad Babaji – daga Ƙaramar Hukumar Funakaye

Adamu Audi, Esq. – daga Ƙaramar Hukumar Funakaye

Dr. Hadi Mohammed – daga Ƙaramar Hukumar Karamar Hukumar Gombe

Ali Yaya Ahmed – daga Ƙaramar Hukumar Karamar Hukumar Gombe

Kabiru Mohammed Mahdi – daga Ƙaramar Hukumar Kwami

Balarabe Musa – daga Ƙaramar Hukumar Kaltungo

Tabitha B. James – daga Ƙaramar Hukumar Kaltungo

Dr Haruna Dadum Hamza, daga Ƙaramar Hukumar Nafada

Ibrahim Mohammed Gombe – daga Ƙaramar Hukumar Nafaɗa

Tahir Adamu Sadiq – daga Ƙaramar Hukumar Shongom

Shuai’bu Chiroma Muhammad – daga Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba

Musa Idi Batari – daga Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba

Gwamna Inuwa Yahaya yana sa ran sabbin Manyan Sakatarorin za su yi amfani da tarin gogewa, ƙwarewa da sanin makamar aiki wajen sauƙe nauyin da aka ɗora musu, yayinda suke bada gudummawa mai ma’ana ga manufar gwamnati na gina ma’aikata masu nagarta, inganci da kuma kwarewa.

Duk naɗe-naɗen sun fara aiki ne nan take.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: NEDC Ta Fara Shirin Kera Sanitary Pads A Gombe Domin Samar Da Sana’o’i
Next Post: Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi

Karin Labarai Masu Alaka

Najeriya Tayi Asarar Kusan Naira Triliyan 1 Sakamakon Harajin Trump Amurka
Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya
Shin Ko Ganawar Zelensky Da Macron Zata Haifar Da ‘Da Mai Ido? Labarai
Wani Jirgi Yayi Saukar Angulu Ba Shiri Najeriya
Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye Afrika
Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu
  • NUJ Ta Kai Ziyarar Jaje GMC Bayan Gobara Ta Lalata Ginin Sashen Talabijin

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gombe Ta Yi Fice A Duniya: Maryam Dan’azumi Ta Lashe Gasar Alƙur’ani Na Ƙasa Da Ƙasa Afrika
  • Wasu Mutane 15 Sun Rasa Rayukan Su A Gabashin Kwango Afrika
  • Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin Afrika
  • Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Yadda Aka Yaudari ‘Yan Kasar Ake Tilasta Musu Ayyukan Bauta Afrika
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa Afrika
  • Inuwa Ya Bukaci A Kara Zuba Jari A Ilimin Sana’o’i Domin Samar Wa Matasa Aikin Yi Afrika
  • Gwamnatin Gombe Zata Inganta Samar Da Wuta Wajen Amfani Da Hasken Rana Kimiya
  • Somaliya: Ba Za Mu Dauki Wulakancin Donald Trump Ba! Sauran Duniya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.