Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnan Jihar Filato Na Shirin Komawa APC
Published: January 26, 2026 at 9:52 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Yayinda a yau Talata jami’iyyar APC a jihar Filato ke shirin karbar gwamnan jahar, Caleb Mutfwang, bayan ya chanza sheka daga jami’iyyar PDP, komitin shirye-shiryen karbar gwamnan yace matakin da gwamnan ya dauka domin hadin kan al’ummar jahar ne da samadda ci gaba.

A taron ganawa da manema labarai a Jos, fadar jaha Filato, shugaban komitin kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai ta Najeriya, Ahmad Idris Wase yace chanza sheka da gwamnan jahar ta Filato yayi shine matakin farko na samun zaman lafiya da ci gaba a jahar da ta sha fama da rikita-rikita.

Gwamnan jahar Filato, Caleb Mutfwang ya sami gagarumin goyon bayan jama’ar jahar a karkashin jami’iyyar PDP, duk da jeka ka dawo da aka yi a kotuna daban-daban, bias cewa jami’iyyar PDP bata da tsari a matakin jaha, kafin zaben dubu biyu da ishirin da uku.

Honarabul Nuru Shehu shine tsohon mai ba gwamnan hajar Filato Caleb Mutfwang shawara a mazabar Jos ta Arewa, yace gwamnan bai nuna dattako ba.

Kafin komawar gwamnan na jahar Filato, Caleb Mutfwang zuwa jami’iyyar APC, an yi ta kai ruwa rana tsakanin ‘ya’yan jami’iyyar, wanda wadansu suka nuna basu kaunar shigansa jami’iyyar.

Alhaji Saleh Abdullahi Zazzaga na daga cikin wadanda suka tsaya kai da fata wajen ganin gwamnan ya tsallaka zuwa APCn yace irin ayyukan da gwamnan yayi shi yasa suka bukaci kasancewarsa a jami’iyya daya da shagaban kasa, ya kara da cewa sun riga sun bashi shugabancin jami’iyyar a jaha da ma tikitin shiga zaben gwamna a dubu biyu da ishirin da bakwai.

A zaben shekara ta dubu biyu da ishirin da uku dai gwamnan, Caleb Mutfwang ya yi fafata da shugaban jami’iyyar APC na yanzu, Farfesa Nentawe Yilwatda a takarar gwamna, wanda masu sharhi ke bada shawarar jira da kallon yadda siyasar jahar zata kasance nan gaba.

Ga Rahoton Zainab Babaji Daga Jos a Najeriya

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/01/AUD-20260126-WA0031.mp3
Siyasa

Post navigation

Previous Post: Sanyi Mai Tsanani Da Dusar Kankara Ya Tsaida Al’amura A Amurka
Next Post: Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas

Karin Labarai Masu Alaka

Mulkin Kama Karya Yazo Karshe a Kasar Bulgaria Siyasa
Samar Da Tsaro A Jihar Kano Ba Sai An Sa Siyasa Ba! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnatin Tinubu Ta Karyata Kafa Kamfanin Gwal A Legas Labarai
Ana Gudanar Da Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnati A Kasar Tunisiya Siyasa
Gwamna Abba Ya Gana Da Kwankwaso Kamun Ganawarsa Da Tinubu Siyasa
Babangida: Hakika Abiola Ya Lashe Zaben Watan Yuni 1993 Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankan Rago A Jihar Neja Labarai
  • ‘Yan-Ta’adda Sun Kara Sace Mutane A Jihar Naija! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya: Ba Don Leken Asiri Muka Tura Jirgin Yakin Mu Ba Afrika
  • Gwamnan Jihar Kano Ya Fice Daga Jam’iyar NNPP Siyasa
  • Kasar Rasha Ta Zargi Ukraine Da Kai Hari Gidan Shugaban Rasha Amurka
  • Salmanu: Ci Gaban Wikki Tourist FC Shine A Gaba Na Wasanni
  • Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.