Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewar tana duba yuwuwar bude makarantu a farkon sabon shekara mai zuwa bayan hutun karshen shekara, yayin da take ci gaba da tantance yanayin tsaro a fadin jihar.
Majiyar mu ta habarto cewa, Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Dr. Muhammad Lawal Rimin Zayam, ya ce akwai yuwuwar makarantu su koma karatu a farkon shekarar 2026 tare da shirya jarabawar zangon farko nan take bayan komawa.
A ranar 23 ga watan Nuwamba, na shekarar 2025 ne Ma’aikatar Ilimi ta bayar da umarnin rufe dukkannin makarantun jihar, har da manyan makarantu, sakamakon yawaitar sace sacen dalibai da ake fama da su a sassan kasa.
A cewar Kwamishinan, lokacin da aka rufe makarantun, saura kimanin makonni biyu ne a kammala zangon karatu da ake ciki.
Ya ce gwamnati za ta yi amfani da wannan damar wajen gudanar da gyar gyare a makaranti jihar domin samar da yanayi mai kyau da aminci ga dalibai lokacin da suka koma Makarantu domin kyautata ilimi.
Kwamishinan ya bayyana cewa shirin da ake yi na komawa makarantu ya yi daidai da shirinSafe Schools Initiative, inda ya kara da cewa yawancin makarantun jihar yanzu suna da katanga domin karfafa tsaro.
Ya kuma shawarci dalibai su ci gaba da karatu a lokacin hutun ta hanyar amfani da Fasahar zamani ta Nigeria e-learning platform, wato tsarin koyo da aka yi amfani da shi a lokacin kulle na COVID-19.
Kwamishinan ya kara da cewa dalibai za su ci gaba da zangon karatu ba tare da wani hutun karshen zangon ba, domin cike gibin lokacin da aka rasa yayin rufe makarantun.


