Jamhuriyar Nijar ta kudiri aniyar rage yawan shinkafa da masara da alkamar da ke shiga kasar daga ketare da kashi 50% kafin nan da shekarar 2027.
Gwamnatin ta Nijar tace wannan wani mataki ne da ke hangen samar wa kasar cikeken ‘yancin kai a fannin cimaka a daidai lokacin da ta ke kokarin katse abin da ta kira ‘’ragowar igiyoyin mulkin mallaka’’ da a ke hasashen su na dabaibaye harakoki da dama.
Wakilin GTA Hausa Amurka ke Magana Souley Moumouni Barma ya aiko mana Cewar, Hekta 21200 ne gwamnatin ta Nijar ta ce ta dauri aniyar bajewa domin fadada aiyukan noman zamani ba’idin hekta 10000 da tuni aka riga aka ga tasirin da suka yi wajen samar da wadatar cimaka a kasar a cewar ministan noma da kiwo kanal Mahaman Alhaji Ousman a yayin da ya ke jawabi a zauren majalissar wakilai ta rikon kwarya CCR.
Ta hanyar wannan tsari da ake saran shimfidawa a jimilce kan hekta 39700 ana hasashen girbe amfani sau biyu a kowace shekara inji ministan wanda kuma ya kara da cewa abu ne da zai bada damar samun a kalla Ton 481000 na shinkafa daga nan zuwa shekarar 2027, lamarin da ka iya rage adadin shinkafar da ke shiga kasar daga waje har ma da marasa da alkama.
Bayanan ministan sun gamsar da ‘yan majalissar kamar su Issa Adam domin a ta su fahimta zartar da kudirin gwamnatin zai samar da sassaucin rayuwa a wajen al’umma.
Galibin jama’ar Nijar sun dogara kan noma da kiwo a matsayin hanyoyin samar wa kansu cimaka sai dai matsaloli masu nasaba da canjin yanayi na haifar da babban gibin amfani, a kowace shekara idan aka kwatanta da abinda ake samu a baya abinda ke zama silar tsadar farashi a kasuwanni.
Hakan yasa shugaban kungiyar kare hakkin masaya ta ADDC Maman Nouri ke yaba wa da shirin da hukumomin suka bullo da shi.
Dam dam da manyan madatsun ruwa ne ake shirin ginawa kari akan wadanda ake da su a baya domin tabbatar da wadatar ruwan da za a yi amfani da shi a aiyukan da aka sa gaba a illahirin jihohi, kamar yadda aka yi tanadin kwararrun ma’aikata da kayan aikin noman zamani a wani bangare na aiyukan da shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi alkawali a kundin manufofinsa, aikin da zai lakume makuddan miliyoyin cfa.


