Gwamnatin jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da samuwar wata ƙungiyar dake lalata tare da cin zarafin fursunoni a Gidan Gyaran Hali na Potiskum.

Mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Abdulsalam Abubakar mai ritaya, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron Majalisar Tsaron Jihar da aka gudanar a ranar Talata a Damaturu.
Abdulsalam ya bayyana lamarin a matsayin babbar cin amana, inda ya ce ana zargin wasu jami’an gidan yari da yi wa wata fursuniya ciki a cikin gidan gyaran halin.
Ya ce hakan na nuna sakaci wajen aiki da kuma rashin kulawa yadda ya kamata, yana mai cewa a ka’ida babu yadda za a yi jami’in tsaro namiji ya shiga sashen mata idan ana sa ido yadda ya dace.
Mai ba da shawarar kan tsaro ya ce, bincike na ci gaba da gudana, inda ya kara da cewa har yanzu ba a tantance adadin jami’an da ke da hannu a lamarin ba, domin ana ci gaba da kama wasu da ake zargi inda ya kara da cewa, al’amarin wata ƙungiya ce mai faɗi, bawai mutum ɗaya ba, kuma akwai masu taimaka musu ciki har da wasu jami’an mata.
Sai dai Abdulsalam ya nuna fatan cewa duk wanda aka samu da laifi a binciken da Hedikwatar Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa ke gudanarwa, za a miƙa shi ga ‘yan sanda domin gurfanar da shi a gaban kotu.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta riga ta kai ƙorafi ga shugabancin Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa da Ma’aikatar Harkokin Cikin gida yana mai jaddada cewa gwamnati na da alhakin kare rayuka, dukiya da mutuncin al’umma.
A game da samar da tsaro lokacin bukukuwan Kirsimeti, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Emmanuel Ado, ya ce an shirya tsaro sosai, inda aka tura jami’ai da dama zuwa wuraren ibada da wuraren shakatawa.
Ya tabbatar wa mazauna jihar, musamman mabiya addinin Kirista, cewa za su gudanar da bukukuwansu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba.


