Gwamnatin Donald Trump na son samar da kungiya mai muhimmanci ta kasuwancin ma’adanai da ‘yan kawancen ta, wadda zata yi amfani da harajin kudin fito don kula da kayyadaddun farashi mafi kankanta, kuma su samu kariya kan yadda kasar China ke cika kasuwa da kaya don dakilai abokan hamayyar kasuwanci.
A ranar Laraba, mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya ce yakin kasuwancin da ake tabkawa a shekarar da ta gabata ya bankado yadda yawancin kasashe suka dogara da ma’aidanai masu muhimmanci da China ke damke da su.
Da yake magana a wata tattaunawa da ministocin kasashen wajen, Vance ya ce Amurka na son kungiyar kasuwancin tsakanin ‘yan kawance zata samar da tabbacin cewa Amurka na da dama kan karfin da take da shi na masana’antu, yayin da kuma take fadada sarrafa kaya a duk fadin yankin.


