Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Hadakar Gwamnatin Najeriya Da Amurka Ne Suka Kai Hari Sokoto
Published: December 26, 2025 at 9:50 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Najeriya ta sanar da nasarar kai hare-haren da aka tsara cikin tsanaki kan wasu manyan sansanonin ’yan ta’addan ISIS guda biyu da ke cikin dajin Bauni, a ƙaramar hukumar Tangaza ta Jihar Sokoto.

A cewar sanarwar da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fitar, an gudanar da harin ne tare da haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Ƙasar Amurka, bayan bayanan sirri sun tabbatar da cewa ’yan ISIS daga yankin Sahel na amfani da wuraren a matsayin wajen taro da shiryawa domin kai manyan hare-haren ta’addanci a cikin ƙasar nan, tare da taimakon wasu ƙungiyoyin t’addanci na cikin gida.

Sanarwar ta ce an kai hare-haren ne tsakanin ƙarfe 12:12 na dare zuwa 1:30 na safiyar Juma’a, 26 ga Disamba, 2025, bayan samun cikakken amincewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR.

An bayyana cewa an gudanar da aikin ne a karkashin tsayayyen tsarin umarni da jagoranci, tare da shigar Rundunar Sojin Najeriya, a ƙarƙashin kulawar Ministan Tsaro, Ministan Harkokin Waje, da Babban Hafsan Tsaro.

Hare-haren sun samo asali ne daga tashar jiragen ruwa da ke yankin Tekun Guinea, bayan dogon nazarin bayanan sirri, shirye-shiryen aiki da bincike na sama.

Jimillar harsasai masu bin tsarin GPS guda 16 ne aka yi amfani da su ta hanyar jiragen sama marasa matuƙa samfurin MQ-9 Reaper, lamarin da ya kai ga kawar da ’yan ISIS ɗin da ke ƙoƙarin shigowa Najeriya ta hanyar yankin Sahel.

Sai dai a yayin aikin, wasu ragowar harsasai sun faɗo a yankin Jabo da ke Ƙaramar Hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto, da kuma a Offa ta Jihar Kwara, kusa da wani otel.

Gwamnati ta tabbatar da cewa babu wani farar hula da ya jikkata a wuraren, kuma jami’an tsaro sun gaggauta killace yankunan.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kawar da duk wata barazanar ta’addanci, musamman daga ƙungiyoyin ta’addanci na ƙetare da ke ƙoƙarin tauye ikon Najeriya da tsaron al’ummarta.

Sanarwar ta ƙara da cewa Najeriya na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙawayenta na dabarun tsaro da abokan hulɗa domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa, tsaron iyakoki da kwanciyar hankali a yankin.

Gwamnati ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa tana da cikakken iko kan tsarin tsaron ƙasa, tare da ƙudirin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, sannan kuma an buƙaci al’umma da su kasance cikin kwanciyar hankali da taka-tsantsan yayin da ake ci gaba da ɗaukar matakan murƙushe duk wata ƙungiyar ta’addanci da ke barazana ga ƙasa.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Ankara Gano Wani Abu Mai Kama Da Abun Fashewa A Jabo Jihar Sokoto
Next Post: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Hadakar Ta Da Amurka Wajen Yakar ‘Yan Ta’adda

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Ya Nada Shugabannin Hukumar NERC Najeriya
Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu Najeriya
Matatar Man Dangote Ta Samu Tagomashi Daga Abokan Hulda Najeriya
Majalisa Ta Sanya Baki Akan Rikici Tsakanin Dangote Da Hukumar Albarkatun Mai Najeriya
Kananan Hukumomi Na Kokarin Karbar Kudadensu Daga Jihohi Najeriya
Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutum 1 Yayinda Mutane 11 Suka Kamu A Jihar Gombe Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Majalisar Dattawa Ta Wanke Janar Christopher Musa A Matsayin Minista Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Wasan Kwallon Kafar Najeriya A Shirye Suke Wasanni
  • Tsohon Alkalin Alkalai A Najeriya Ya Rasu Yana Da Shekaru 71 Labarai
  • Gwamna Ahmad Aliyu Na Jihar Sokoto Ya Gabatar Da Kasafin Fiye Da Naira Biliyan 700 Labarai
  • ‘Yan Sanda Sunce Mutum Daya Ne Yakai Hare-Haren Jami’ar Brown Da Kuma Na MIT Boston Amurka
  • Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai
  • Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan Labarai
  • Bana Ba Harka Ga ‘Yan-Wasan Kwallon Kafar Najeriya Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.