Mutane 9 sun rasa rayukansu, wasu akalla 10 suka ji rauni a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan wata mashaya da asubahin lahadi a kasar Afirka ta Kudu.
Wannan lamarin ya faru da misalin karfe 1 na dare a garin bakar fata na Bekkersdal dake da tazarar kilomita 46 a yamma da birnin Johannesburg, wannan shine mummunan harin bindiga na biyu da aka kai cikin kasar a makonni ukun da suka shige.
Wasu ’yan bindiga su 12 cikin wasu moto biyu, sun bude wuta a kan mutanen dake shakatawa a wannan mashaya mai suna KwaNoxolo dake unguwar Tambo a garin na Bekkersdal, suka kuma ci gaba da bude wuta kan jama’a a yayin da suke tserewa daga wurin.
‘Yan sandan Afirka ta Kudu suka ce wasu daga cikin mutanen suna tafiyarsu ne kawai a kan titi a lokacin da ‘yan bindigar suka bude musu wuta.
Kwamishinan lardi mai kula da Gauteng, MNanjo janar Fred kekana, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AP a wurin da wannan lamari ya faru cewa ‘yan bindigar, wadanda wasunsu suka rufe kai da fuskarsu da kyalle, sun yi amfani da bindiga samfurin AK-47 guda daya da wasu kananan bindigogi da yawa.
‘Yan sanda ba su bayar da bayanin mutanen da aka kashe ko aka raunata ba, amma kakakin rundunar sandan, Birgediya Brenda Muridili, ta ce akwai wani direban tasi wanda ya ajiye fasinja ke nan zai bar wurin sai maharan suka rutsa da shi, kuma suka kashe shi.


