Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Hukumar ICPC Ta Gayyaci Dangote
Published: December 21, 2025 at 6:58 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

ICPC ta gayyaci Dangote kan zargin biyan kuɗin makaranta dala miliyan $7 ga tsohon shugaban NMDPRA.

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (ICPC) ta gayyaci ɗan kasuwa Aliko Dangote domin ya ba da ƙarin bayani kan ƙorafin da ya shigar kan tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA), Alhaji Farouk Ahmed.

Ana sa ran Dangote zai bayyana da kansa ko kuma ya turo lauyansa, Ogwu Onoja (SAN), ranar litinin yayin da ICPC za ta fara binciken ƙorafin a hukumance.

Rahotanni sun ce hukumar ta kafa wani kwamitin manyan masu bincike a ranar Juma’a domin gudanar da binciken, kuma ta bukaci Dangote ya gabatar da dukkan hujjojin da ke hannunsa ga hukumar yaƙi da cin hanci.

Dangote ya zargi Farouk da cin hanci da almundahana, ciki har da kashe miliyoyin daloli wajen karatun ‘ya’yansa huɗu a makarantu masu tsada da ke Switzerland.

Har ila yau, ɗan kasuwar ya zargi Farouk da yin zagon kasa ga tattalin arziki wajen raunana tace man fetur a cikin gida, ta hanyar haɗa baki da ‘yan kasuwar waje da masu shigo da mai, da ya ci gaba da ba su lasisin shigo da main fetur.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Hukumar Tsaron Civil Defence A Gombe Ta Samar Da Jami’ai Don Tabbatar Da Tsaro A Bukukuwan Karshen Shekara
Next Post: An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade

Karin Labarai Masu Alaka

Yohanna YD Buru: Makon Haɗin Kan Addinai Ya Ƙarfafa Ilimin Zaman Lafiya A Najeriya Labarai
An Samar Da Dala Kusan Biliyan Biyu Don Yakar Polio Labarai
Takaddama Ta Barke Tsakanin Lebanon Da Isra’ila Akan Bakin Iyaka Labarai
Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Zata Tabbatar Da Tsagaita Wuta A Kwango Afrika
Gobara Ta Lalata Shaguna Da Gidajen Abinci A Gombe Labarai
Tsohon Shugaban Brazil Bolsanaro Zai Tafi Gidan Yari Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • An Gudanar Da Addu’oi Ga Mutane 16 Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe a Australiya Tsaro
  • Farashin Zinari Yayi Tashin Gwauron Zabi Amurka
  • Hukumomin Taliban Sunce A Shirye Suke Domin Sulhu Afrika
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwar da Mutane a Jihar Gombe Tsaro
  • Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe Labarai
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Labarai
  • Gobara Ta Tashi A Makarantar Koyon Jinyar Dabbobi Dake Jihar Kano Najeriya
  • Mayakan M23 Sun Tsagaita Wuta A Gabashin Kwango Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.