Hukumomi a Sri Lanka sun ce a ranar Jumu’a zasu raka wani jirgin yakin ruwa na Iran zuwa Tasha, kuma zasu kwashe ma’aikatan jirgin su 208 zuwa wani sansani. Wannan ya biyo kwana 2 bayan da jirgin ruwan Amurka ya nutsar da wani jirgin yakin Iran a wajen.
Shugaban kasar Sri Lanka, Anura Kumara Dissanayake, ya ce kasar sa na da nauyin kare hakki, wajen samarwa da mutanen masauki, yayin da yaki tsakanin Isra’ila, Amurka da Iran ke ci gaba da tsamari, yana kawo hargitsi ga kasuwannin hannun jari, yana kuma rikirkita kasuwanci da tafiye-tafiye.
An ga matukan jirgin ruwan Iran dauke da jakunkuna, yayin da suka isa Sri Lanka, wasu hotunan kuma sun nuna jiragen kwale-kwale na Sri Lanka na karasawa zuwa inda jirgin Iran din yake.


