Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Iran Tace Dole A Tsagaita Wuta A Lebanon Kafun Fara Shawarwari
Published: April 11, 2026 at 11:22 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

A ranar  juma’a Iran tace tilas a sakamarta kadarorinta, kuma a tsagaita wuta a Lebanon, kamun ta fara shawarwari da Washington, mataki da ya jefa zaman sulhu da za’a fara yau Asabar, cikin rashin tabbas.

Kakakin majalisar dokokin kasar Mohammed Baqeer Qaibaf ya fada a shafinsa a dandalin X cewa, wadannan bukatu biyu dama an amince da su a magana da suka yi da Washington, saboda haka ba za’a fara shawarwari ba har sai an cikata alkawuran, yayinda ake ci gaba da takaddama kan ainihin sharuddan tsagaita wuta.

Shi ma ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi, ya jaddada haka, ya bukaci da a kawo karshen farmakin da Isra’ila take kaiwa a Lebanon. Ana sa ran duka jami’an biyu na Iran za su kasance a wajen zaman shawarwari da za’a yi, kamar yadda wasu majiyoyi biyu a Pakistan suka fada.

Kodashike babu wani martani nan take daga fadar White house, shugaban Amurka Donald Trump ya fada a wani sako da ya wallafa a shafinsa dandalin sada zumunta da ake kira Truth Social, dalili daya da ya sa har yanzu Farisawan suke da rai shine domin a kulla yarjejeniya da su.

Shugaba Trump wanda bai maida martani kai tsaye kan bukatun da Iran ta gabatar ba, ya gayawa wata jaridar Amurka da ake kira New York Post, cewa, jiragen ruwan yaki ana sake musu shiri da albarusai masu kwari domin su ci gaba da kai farmaki kan Iran, muddin shawarwarin sulhu da za’a yi Iran a Pakistan ya ci tura.

Mataimaki shugaban Amurka JD Vance wanda zai jagoranci tawagar Amurka zuwa taron, yace yana fatan za’a sami kyakyawar sakamakon taron da za su yi, ya kara da cewa, “Idan kuma za su kokarin su yaudare mu, za su fuskanci turjiya daga tawagar.”

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Hari Da Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Mutane Da Dama A Darfur
Next Post: Mataimakin Shugaban Amurka Ya Sauka A Islamabad Domin Tattaunawa

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Mutunta Hukuncin Kotun Ƙoli Kan ’Yancin Kuɗin ƙananan Hukumomi Labarai
Mutane 27 Sun Rasa Rayukan Su A Najeriya Afrika
Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Najeriya Ta Tabbatar Da Kyautata Rayuwar Mambobin ta Labarai
An Kama Maharan Bom Din Maiduguri Tsaro
Za’a Jima Ana Fama Da Tsadar Farashin Mai Afrika
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Senegal Yaki Amincewa Da Hukuncin CFA Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jirgin Hakar Mai Daga Turkiyya Ya Isa Mugadishu
  • Farashin Mai Ya Doshi Dala 100 Kowacce Ganga
  • Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye
  • Mataimakin Shugaban Amurka Ya Sauka A Islamabad Domin Tattaunawa
  • Iran Tace Dole A Tsagaita Wuta A Lebanon Kafun Fara Shawarwari

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Faransa Zata Bunkasa Nukiliyarta Afrika
  • Thailand Da Cambodia Sun Fara Tattauunawa Kan Batun Tsagaita Wuta Labarai
  • An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
  • Iran Tayi Allah Wadai Da Kai Hari Cibiyar Pars Afrika
  • Wani Bayahude Ya Harbe Bafalatsine Dan Shekaru 16 Tsaro
  • Ministan Sufurin Najeriya Ya Ajiye Mukaminsa Domin Takarar Gwamna Afrika
  • Kudi Sunfi Rayuwar Mutum Muhimmanci A Asibitocin Najeriya Kiwon Lafiya
  • Hukumar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Tace Isra’ila Ce Ta Kashe ‘Yan Jarida Kashi Biyu Bisa Uku Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.