Ana samun karin kasashen dake fitowa suna yin Allah wadarai da amincewar da kasar Isra’ila ta yi da yankin Somaliland na kasar Somaliya a zaman kasa mai ‘yanci.
Ba a san dalilin da ya sa isra’ila ta fito ranar Jumma’a tana fadin cewa ta amince da Somaliland a zaman ‘yan tacciyar kasa ba, amma kuma a farkon shekarar nan jami’an Amurka da na Isra’ila sun fada ma kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa Isra’ila ta tuntubi jami’an yankin na Somaliland, a kan ko zasu karbi Falasdinawa na yankin Gaza, a wani bangare na shirin Shugaba Trump a wancan lokaci na sake tsugunar da mutanen Gaza a wani wuri kuma tuni dai Amurka ta yi watsi da wancan shirin nata.
Wata sanarwar hadin guiwar da kasashe fiye da 20 tare da kungiyar kasashen Musulmi ta duniya OIC suka bayar ta yi watsi da wannan amincewa da isra’ila ta ce ta yi da yankin na Somaliland a zaman kasa mai cin gashin kai, ganin irin yadda hakan zai yi mummunar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Yankin Somaliland ya bayyana ballewa daga Somaliya tun shekarar 1991, amma duk da cewa yana da gwamnati da takardar kudin sa daban, babu wata kasa a duniya da ta taba yarda da shi a zaman kasa.
Sanarwar kasashen ta kuma nuna rashin yarda ko miskala zarratin, da duk wani matakin da Isra’ila zata ce zata dauka dangane da wannan, wajen korar Falasdinawa karfi da yaji daga gidaje da garuruwa da yankunan su.
Ita ma kasar Sham, ko Syria, tayi tur da wannan mataki na Isra’ila a wata sanarwa dabam da ta bayar.
A ranar asabar, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da sanarwa tana jaddada ci gaba da mutunta kasar Somaliya wadda yankinta ya hada da yankin na Somaliland.
Gwamnatin tarayyar Somaliya ta fito ran jumma’a da kakkausar harshe tana yin tur da wannan matakin na Isra’ila da ta ce haramun ne.
Shi ma shugaban Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, yace duk wani matakin gurgunta diyaucin Somaliya na iya haddasa fitina a nahiyar.


