Wasu tsirarrun Jami’an shige da fice na Afirka ta Kudu sun yi amfani da matsayin su don cimma burin su ta hanyar karban kudade a wurin mutane suna sama musu visa da takardun zama a kasa, kamar yadda wani binciken gwamnati ya bankado a Ranar Litinin.
Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya bada umurnin yin binciken da ya gano wannan badakala da ke yi na bada visa tun daga shekarar 2004 har zuwa 2024, tun kafin gwamnatin hadin guiwa ta yanzu ta karbi mulki. Binciken ya gano cewa an mai da sashen na shige da fice kamar wata kasuwa, ka biya a siyar maka.
Ba’a bayyana sunan jami’an da ake zargi ba, amma hudu daga cikin su sun karbi jimillan kudi Rand miliyan 16, wanda yayi daidai da dala miliyan daya, kai tsaye zuwa bankunan su. Daya daga cikin su ya gina katon gida, yayin da wasu kuma suka sayi kadarori da dama, a cewar sashen bincike na musamman na kasar.


