Jihar Ekiti ta zama jiha ta farko a Najeriya da ta aiwatar da dokar gudanar da Haraji ta Najeriya, bayan Gwamna Biodun Oyebanji ya sanya hannu kan dokar gudanar da kuɗaɗen shiga ta jihar Ekiti, na 2025.
Haka nan, ya amince da kasafin kuɗin jihar na 2026 mai ɗauke da naira biliyan 415.57, wanda aka yi wa lakabi da “Kasafin Gudanarwa Mai Dorewa.”
Gwamnan ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta tabbatar da gaskiya, ingantaccen shugabanci da sauƙin biyan haraji , tare da kawar da almundahana a harkar tattara kuɗaɗen shiga.
Dokar ta bai wa hukumar harajin cikin gida ta jihar Ekiti cikakken ikon tattara kuɗaɗen shiga, tantance kwararrun wakilan haraji da gudanar da gurfanarwa a kotu.
Segun Adesokan, Sakataren zartarwa na hukumar haɗin gwiwar haraji, ya yaba wa Ekiti kan jagoranci da ta ɗauka, yana mai cewa aiwatar da dokar na nuna jajircewa wajen ƙwarewa da ‘yancin kai a harkar tattara kuɗaɗen shiga.
Kasafin kuɗin na shekarar 2026 ya mai da hankali kan kammala ayyukan ci gaba, samar da abinci, arziki da gina ababen more rayuwa, inda kashi 53% aka ware wa kashe kuɗaɗen yau da kullum, yayin da kashi 47% aka ware wa ayyukan raya kasa.


