Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Jihar Gombe Ta Saka Hannu Kan Yarjejeniya Da Kamfanonin Tunisiya
Published: February 12, 2026 at 11:25 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya gana da tawagar masu zuba jari da abokan hulɗar ci gaba a ƙarƙashin ƙungiyar rukunin kamfanonin ƙasar Tunisia Masu fafutukar kawo ci gaba a Afirka (Tunisia Consortium for African Development, TUCAD) don samar da haɗin gwiwa mai muhimmanci da kuma buɗe sabbin damammakin zuba jari a fannoni masu mahimmanci ga ƙudurin ci gaban jihar.

Taron, wanda aka gudanar a masauƙin gwamnan dake Abuja, wanda Jakadan Tunisiya a Najeriya, Mohsen Antit ya halarta, ya mayar da hankali ne kan manyan ayyuka masu gwaɓi a muhimman fannoni da suka haɗa da samar da ruwa da wutar lantarki, da makamashi mai tsafta, da sufuri da kuma muhimman kayayyakin more rayuwa ta fuskar wasanni.

Wannar yarjejeniya ta zo ne kafin wata gagarumar ziyarar da ƙungiyar za ta kawo jihar Gombe don ganowa, tsarawa da kuma fara aiwatar da ayyukan haɗin gwiwa tsakanin ɓangarorin biyu.

An cimma wannan haɗin gwiwa ne bisa sahalewar Kamfanin Sadarwa na Afirka, SARL Limited, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ahmed Shuaibu Gara Gombe, bisa ci gaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar Gombe na jawo hankalin masu zuba jari na ƙasashen duniya da ƙwararrun abokan hulɗa don tallafawa ƙudurinta na kawo sauyi.

Mataimakin Shugaban rukunin kamfanonin, Issam Ben Youssef, wanda ya jagoranci tawagar ta TUCAD, yace an tsara wannar yarjejeniya ce don samo ƙwarewar fasaha ta Tunisiya da ƙarfin zuba jari tare da muhimman ƙudurorin jihar Gombe a fannin ci gaba.

“Manufarmu ita ce mu yi amfani da gogewar da Tunisiya ke da shi a fannin ababen more rayuwa, makamashi, tsarin samar da ruwa da ci gaban masana’antu don tallafawa ƙudurin ci gaban jihar Gombe, yayin da muke gina haɗin gwiwa mai ɗorewa da kuma amfanar juna,” in ji shi.

Manyan shugabanni da manyan jami’an gudanarwa na kamfanonin daban-daban dake ƙarƙashin rukunin, sun yi ta gabatar da bayanai daki-daki kan ƙwarewarsu ta fasaha, da ayyuka da kuma fannoni na musamman, inda suka bayyana hanyoyin haɗin gwiwa masu muhimmanci wajen aiwatar da manyan ayyuka masu tasiri da ɗorewa.

A jawabinsa, Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da tawagar tare da sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na samar da kyakkyawan yanayi mai ɗorewa, na gaskiya kuma mai sauƙin zuba jari wanda ke tallafawa harkokin zuba jari na dogon lokaci waɗanda ke da tasirin da ake buƙata.

Yace jihar Gombe tana ba da fifiko sosai wajen faɗaɗa kayayyakin more rayuwa, makamashi mai tsafta, samar da wadataccen ruwa, bunƙasa masana’antu da kuma gina jama’a a matsayin manyan abubuwan dake faɗaɗa tattalin arziki, da samar da ayyukan yi da kuma ci gaban da ya shafi kowa da kowa.

“Kofofin jihar Gombe a buɗe suke ga masu zuba jari, musamman a tsarin Afirka da Afirka. Dabarun ci gabanmu ya dogara ne akan ababen more rayuwa, bunƙasa makamashi, samar da wadataccen ruwa, noma da ci gaban masana’antu. Muna sha’awar yin aiki tare da abokan hulɗa masu aminci waɗanda ke da hangen nesa iri guda da mu,” in ji Gwamnan.

Gwamna Inuwa Yahaya ya tabbatarwa tawagar cewa gwamnatin jihar Gombe a shirye take ta samar da goyon bayan da ya dace kama daga hukumomi, da goyon baya na manufofi da kuma sauƙaƙa dokoki don tabbatar da aiwatar da ayyukan da aka amince da su a kan lokaci.

Taron ya ƙarƙare da sanya hannu kan yarjeniyoyin fahimtar juna (MoUs) tsakanin Gwamnatin jihar Gombe da Rukunin Kamfanonin na Tunisiya, inda aka tsara fannonin haɗin gwiwa da kuma shimfida harsashi mai ƙarfi don haɓaka ayyuka da aiwatar da su.

Kwamishinan Makamashi da Ma’adinai Sanusi Ahmed Pindiga, da Kwamishinan Muhalli, Ruwa da Gandun Daji, Mohammed Saidu Fawu ne suka sanya hannu kan yarjeniyoyin a madadin Gwamnatin jihar Gombe, yayin da Issam Ben Youssef da sauran manyan jami’ai suka sanya hannu a madadin kamfanoninsu.

Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a, Barrister Zubairu Muhammad Umar, ya sanya hannu a matsayin shaida ga gwamnati, yayin da Alhaji Ahmed Shuaibu Gara-Gombe ya kasance shaida a madadin rukunin kamfanonin na Tunisia.

Mataki na gaba na wannar yarjejeniya shine ziyarar da rukunin kamfanonin na TUCAD za ta kawo jihar Gombe don nazari da tantance shirye-shiryen jihar, da nufin zurfafa bincike kan yadda za a aiwatar da ayyukan haɗin gwiwan, da nazarin yiwuwar ayyukan da kuma saurin sauyawa daga yarjejeniyoyi zuwa aiwatarwa.

Ana sa ran wannan haɗin gwiwa zai ƙarfafa ƙarfin Jihar Gombe a fannin samar da ruwa, da makamashi mai tsafta, da haɓaka kayayyakin more rayuwa a fannin sufuri da raya birane, yayin da zai buɗe sabbin hanyoyi don ci gaban kamfanoni masu zaman kansu, da musayar fasaha da kuma samar da ayyukan yi.

Kimiya, Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Anyi Sallar Rokon Ruwa A Saudiya
Next Post: Gwamnatin Sokoto Tabada Umarnin Biyan Albashin Watan Fabrairu

Karin Labarai Masu Alaka

Bisa Alamu Hadinkan Kasashen Yankin Sahel Zai Haifar Da Nagarta Afrika
‘Yan Tawayen Kasar Kwango Ne Suka Kai Hari Filin Jirgin Saman Kisangani Labarai
Ana Cigaba Da Bincike Game Da Mutuwar Matar Da Likita Ya Manta Almakashi A Cikinta A Kano Najeriya
Burkina Faso Ta Sako ‘Yan Najeriya 11 Najeriya
Ga Fili Ga Doki Najeriya
‘Yan Bindiga Sun Kashe Dan Gaddafi A Gidansa Dake Kasar Libya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Da Gwamnan Minnesota Zasu Sassautawa Bakin Haure Amurka
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Anyi Taho Mugama Tsakanin ‘Yan Sandan Turkiyya Da ‘Yan Kungiyar ISIS Afrika
  • CAF, Zata Ci Tarar Wasu Kasashe AFCON 2025 Wasanni
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha: Tura Sojojin Birtaniya Ukraine Zai Kara Ta’azzara Yaki Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Hana Demokraɗiyya A Najeriya Siyasa
  • Kasar Israela Zata Gina Sansani A Gaza Afrika
  • Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.