Mutane 11 Sun Tsallake Rijiya da Baya a wani Hatsarin Jirgin Sama da ya auku a birnin Kano
Mutane 11 sun kubuta daga wani mummunan hatsarin jirgin sama da ya faru a safiyar Lahadi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, da ke birnin Kano.
Jirgin mallakin kamfanin Flybird, wanda ya taso daga Abuja, ya gamu da matsala yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jirgin.
Duk da hatsarin, babu wanda ya rasa ransa ko jikkata a cikin fasinjojin 11 da ke cikin jirgin.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama wayo (NCAA) ta ce an fara bincike kan musabbabin hatsarin, yayin da hukumomi ke ɗaukar matakan tabbatar da tsaro da lafiyar matafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa, shigowar gajimare da kuma wahalar hangen hanya na iya kasancewa cikin abubuwan da suka janyo lamarin.


