Wani Jirgin sama kirar Cessna 172 ya yi hatsari a filin jirgin saman Owerri
Wani jirgin sama kirar Cessna 172 na kamfanin Skypower Express ya yi hatsari da yammacin ranar Talata a Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe da ke Owerri, Jihar Imo, bayan da matukan jirgin suka sanar da shiga yanayin gaggawa.

Jirgin, mai lambar rajista 5N-ASR, yana kan hanyarsa daga Kaduna zuwa Fatakwal, amma aka sauya masa hanya zuwa Owerri, Mutane huɗu ne ke cikin jirgin, kuma babu wanda ya rasa ransa.
Hukumar Binciken Tsaron Jiragen sama ta Najeriya (NSIB) ta ce ba a samu gobara ba, kuma an ci gaba da gudanar da harkokin jirage a filin.
Hukumar ta fara bincike kan lamarin, tana mai bayyana juyayi ga kamfanin jirgin.


