Kamfanin harhada magunguna a Afirka ta kudu da ake kira Aspen, ranar talata ya bada labarin faduwa a cinikayyarsa na rabin shekara da kashi 21 cikin dari, ya aza laifin haka kan garambawul ko ko ayyukan daidaito, duk da haka kamfanin Aspen yana hasashen samun riba sosai a wannan shekara.
Domin ya rage yawan kudi da yake kashewa a tafiyar da ayyukansa kamfanin Aspen yana sake fasali a rassansa da suke janyo masa hasara a Faransa da kuma Afirka ta kudu, inda kamfanin yake hada magunguna da suka hada da allura. Wannan garambawul na baka safai ba, ya janyowa kamfanin Aspen hasarar dala milyan 42 da dori.
Ganin galibin masu harhada magunguna sun gwammace suyi aikin a Amurka domin kaucewa haraji, saboda haka kamfanin ya zamanto ba ya samun kwantiragi, kamar yadda shugaban kamfanin Stephen Sa’ad ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.


