A ranar Laraba ne dai a kasar Afrika ta Kudu aka gayyaci sabon jakadan Amurka don yin bayani, in ji ministan harkokin wajen kasar, yayin da ake ci gaba da samun baraka ta diflomasiyya kan manufofin ketare da gwamnatin Trump ta bayyana a matsayin nuna kyama ga Amurka da manufofin cikin gida da ta kira na kin jinin bakake.
An gayyaci jakada Leo Brent Bozell na III ne bayan ya yi jawabi a taron shugabannin ‘yan kasuwa a ranar Talata, inda ya kalubalanci gwamnatin Afirka ta Kudu game da alakar diflomasiyya da Iran da kuma tabbatar da ka’idojin aikinta na nuna wariyar launin fata a gaban sauran kabilu.
Rikicin dai ya kara kamari ne tsakanin tsofin abokan kawance tun bayan da Shugaba Donald Trump ya koma kan karagar mulki.
Dangantaka ta koma mafi ƙanƙanta tun bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata, ko kuma farar fata, a 1994. Trump na sukar gwamnatin Afirka ta Kudu da Baƙar fata ke jagoranta.


