Kamfanin ByteDance na China, da yake mallakar Tik-Tok ya sanya hanu kan yarjejeniyr sayarda fiye da kashi 80 cikin dari na kadarorin Tik-Tok a Amurka zuwa ga masu zuba jari a Amurka dana ketare, domin kaucewa haramtawa kamfanin gudanarda ayyukansa a Amurka, kamar yadda shugaban kamfanin Shou Zi Chew ya shaidawa ma’aikatan kamfanin jiya Alhamis.
Wannan yarjejeniyar babban mataki ne wajen warware rashin tabbas dangane da ci gaba da aikinsa a Amurka, domin tun zamanin wa’adinsa na farko, shugaba Trump ya nemi hana kamfanin ci gaba da aikinsa, inda Amurkawa samada milyan 170 suke amfani da Tik-Tok.
Yarjejeniyar wacce ake sa ran kammala ta ranar 22 ga watan gobe, zata kawo karshen yunkurin shekara da shekaru da hukumomi suke yi na neman tilastawa kamfanin ByteDance ya janye aiki anan Amurka saboda fargaba ta fuskar tsaro.


