Kasar Botswana tana shirin bude ofishin jakadanci a kasar Rasha, kuma ta gayyaci masu zuba jari na Rasha da su hada kai da ita wajen hakar ma’adinai da duwatsun daiman a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Rasha na TASS ya ambaci ministan harkokin wajen Botswana, Phenyo Butale, yana fadin cewa kasarsa ta fi kowacce tasirin zuba jari a saboda kwanciyar hankalin siyasa da na tattalin arziki.

Rasha tana ci gaba da kokarin karfafa huldodinta a nahiyar Afirka a yayin da take takun-saka da kasashen yammaci.
Kasar Botswana tana samun kashi Daya bisa uku, na kudaden shigarta daga duwatsun daiman, kuma shine ke samar mata da kashi uku cikin 4 na kudaden musanya na kasashen waje.


