Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

China Ta Dawo Da Harajin Magungunan Hana Haihuwa
Published: January 3, 2026 at 9:38 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 3, 2026

Daga ranar 1 ga watan janairu, China ta kakaba haraji kan dukkan magunguna da wasu kayan jima’i da zasu iya hana mace daukar ciki, da zummar kwadaitawa ‘yan kasar haifuwa, yau fiye da shekaru 30 China ta dauke haraji kan irin wadannan kayayyaki.

Daga yanzu kororon roba ko Condom da turanci da sauran kayayyaki na jima’i da za su iya hana mace daukar ciki, za a biya haraji VAT kashi 13 cikin dari kamar dai harajin da ake biya idan aka yi ciniki.

Kasar Sin, tana daukar wannan matakin ne yayinda hukumomin kasar dake Beijing suke kokarin bunkasa hayayyafa, a kasar ta biyu a karfafin tattalin arziki, kuma yawan al’umar kasar shekaru uku ajere yana kara ja’da baya, kuma kwararru suna gargadin cewa lamarin zai dore.

Manyan jami’an kasar a wani taro game da harkokin tattalin arziki da aka yi cikin watan jiya, sunyi alkawarin za su “karfafa auratayya da renon yara,” domin ta sami daidaito kan hayayyafa a kasar.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Kasar Habasha Ta Cimma Matsaya Da Masu Binta Bashi
Next Post: Babu Dabbar Da Zata Sake Shiga Amurka Daga Mexico!

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisar Wakilai Tayi Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Gombe Labarai
Zamu Hada Kai Mu Yaki Cutar Shan’inna (Polio) Labarai
Tawagar Shirya Gasar Kwallon Sarakuna A Gombe Ta Ziyarci Masarautun Jihar Labarai
An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza Labarai
Kamfanin NNPC Yana Tattaunawa Da Wani Kamfanin Kasar China Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • ‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha Afrika
  • Kasashen Mali Da Burkina Faso Sun Haramtawa Amurkawa Shiga Kasashen Afrika
  • Ba Mamaki APC Ta Kafa Tarihi A Ranar Litinin Najeriya
  • Sarkin Musulmi Yayi Magana Game Da Matsalar Tsaron Kasar Tsaro
  • Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Gombe Ta Aza Tubalin Gina Sakatariyar Gundumomin Cigaba (LCDAs) Labarai
  • Akwai Yiwuwar Shugaban Ƙasar Afirka Ta Tsakiya Touadera Yasamu Nasara A Karo Na Uku Afrika
  • Ga Fili Ga Doki Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.