A ranar Alhamis kasar Congo tace ta kawo karshen cutar kyandar biri (monkey pox) da kasar ta shafe shekaru biyu tana fama da, wadda kuma tayi sanadin rayukan mutane fiye da 2,200.
Ministan lafiya Roger Kamba, ya shaidawa manema labarai cewa gwamnati tayi kudurin cewa barkewar cutar ta kau, kuma a yanzu ba’a bukatar daukan matakin gaggawa.
Congo ta kasance kasar da barkewar cutar da ake saurin kamawa ta fara bulla, wadda kuma ta watsu zuwa makwabtan kasashe a shekarar 2024, abinda ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana ta a matsayin hatsari ga lafiya me bukatar daukan matakin gaggawa a daukacin duniya. Hukumar ta cire wannan matsaya a watan Satumbar bara.
Cibiyar kula da rigakafin cututtuka ta Afirka tace an samu fiye da mutane 161,000 da ake zaton sun kamu da cutar ta kyandar biri, lokacin da cutar ta barke tsakanin shekarar 2024 zuwa wannan shekarar, inda aka tabbatar da mutane 37,000 suna dauke da ita ta hanyar gwaji.


