Gambia ta gayawa alkalai a babbar kotun duniya ta MDD cewa Myanmar ta yunkurin gamawa da musulmi ‘yan Rohingya marasa rinjaye, kuma ta jefa rayuwarsu cikin ukuba, a wata babbar shari’a inda ta zargi kasar da kisan kare dangi.
Wannan itace shari’a ta farko kan kisan kiyashi da babbar kotun zata saurara a fiye da shekaru 10, sakamakon shari’ar zata shafar ba kadai a Myanmar ba, watakil hukuncin ya shafi karar da Afirka ta kudu ta shigar kan Isra’ila kan zargi kisan kiyashi kan Falasdinawa, da ta kai gaban kotun sauraron laifuffukan yaki dangane da yakin da Isra’ilan take yi a Gaza.
Ministan shari’ar Gambia Dauda Jallow, ya gayawa alkalan kotun cewa ‘yan Rohingya mutanen kirkiri wadanda suke da buri zaman cikin lumana da mutunci, kuma yace “an auna gamawa da su baki daya.”
Myanmar ta musanta zargin kisan kare dangin, haka ita ma Isra’ila a waccar shari’ar lauyoyin ta musanta zargin kisan kiyashi, suna masu cewa. Afirka ta kudu tana wasa ne ko reni ga dokoki da suka shafi kisan kare dangi.


