Ma’aikatar harkokin kudi a Habasha tace kasar ta cimma kwarya-kwaryar yarjejeniya da masu binta bashi na dala bilyan daya a shekarar 2024, mataki da yake da muhimmanci wajen sake fasalin bashin dake kanta.
Duk da haka akwai bukatar Habasha ta amince da sharuddan bashin da za’a sabunta, kan rancen da ta kasa biya, a shawarwari da zata gudanar da babban kwamitin gudanarwa kan harkokin bashin.
Ma’akatar ta fada cewa ta sanarda asusun bada lamuni na duniya watau IMF yarjejeniyar, da kuma babban kwamitin gudanarwa kan basussuka, tace tana dakon martanin su.
Habasha dake gabashin Afirka, ta kasa biyan bashinta na kasa da kasa a shekara ta 2023, ta gwammace ta sake sabunta yarjejenyar, kamar yadda hukumomin kasa da kasa suka tsara kan dukkan basussuka walau tsakanin kasashe biyu ko fi.


