Kasar Ukraine ta yabawa tarayyar turai bisa hukuncin da ta yanke na bata bashin euro biliyan 90, don taimaka mata zuwa nan da shekara, ko da kungiyar ta kasa cimma matsaya wajan samar mata da kudi daga kadarorin Rasha da aka rike.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce tarayyar turan ta sauka ne daga niyyar ta na amfani da kadarorin Rasha da aka rike ne, saboda sun san zasu fuskanci mummunan martani.
Akwai bukatar taimakawa Ukrain da kudi sosai, saboda idan tarayyar turai bata taimaka mata ba, asusun ta zai yi karaf nan da tsakiyar shekara mai zuwa, kuma zata iya zama kashin baya a yakin ta da Rasha, wanda tarayyar turai take fargabar zai iya matsowa kusa da su.


