Kasashen Thailand da Cambodia sun amince da shirin tsagaita wuta ranar Asabar a karo na biyu a cikin watannin baya bayan nan, bayan kazamin yaki da kasahen biyu makwabtan juna suka gwabza, a yankin kudu maso gabashin Asia.
Shirin tsagaita wutar yana aiki, kamar yadda kakakin ma’aikatar tsaron Thailand Admiral Suran Kongsiri ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters, sa’o’I biyu bayan shirin tsagaita wutar ya fara aiki.
Ma’aikatar tsaron Cambodia bata bada wata sanarwa kan artabu da aka samu ba in banda wani farmaki da ta ce Thailand ta kai a safiyar ranar Asabar, gabannin yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki.
Yarjejeniyar tsagaita wutan, da ministocin harkkin tsaron kasashen biyu suka sanya hanu akai, ya kawo karshen yaki da kasashen biyu suka gwabza na tsawon kwanaki ashirin wadda ya halaka mutane 101, ya tilastawa mutane fiye da rabin milyan daga duka sassan kasashen biyu barin muhallansu.
Kasashen biyu sun fara yaki ne a farkon wannan wata, bayan rushewar yarjejeniyr tsagaita wuta ta farko da shugaban Amurka Donald Trump tare da takwaran aikinsa na Malaysia Anwar Ibrahim suka shiga tsakani aka kulla.


