Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Ateta na kokarin kafa wani sabon tarihi na lashe kofin firimiya karon farko cikin shekaru 24.
Arsenal ta kara tazaran maki Bakwai tsakanin ta Manchester City a gasar firimiya lig na kasar Ingila a bana.
Wannan lamari na zuwa ne bayan da Arsenal ta ci gaba da nuna kwazo a fafatawar neman lashe kambun firimiya lig bayan ta samu nasara a daren Laraba, inda ta doke Brighton & Hove Albion da ci 1-0.
Ita kuma, Manchester City ta yi kunnen doki 2-2 da Nottingham Forest, a gida sakamakon da ya bai wa Arsenal damar kara tazarar maki tsakaninta da babbar abokiyar hamayyarta zuwa maki bakwai.
Arsenal ta buga wasaninta na mako 30 inda take da maki 67, ita kuwa Manchester city ta fafata a wasaninta na mako na 29, inda ta ke da maki 60, Arsenal tana da saura wasanni takwas kacal ta kammala gasar firimiya lig na bana yayin da Manchester city ta ke da ragowar wasaninta Tara ta kammala. cikin wasanin manyan kungiyoyi biyu zasu fafata a tsakanin su
Arsenal ta samu kwarin guiwa sosai bayan wasan mako na 30 in har zata yi kokarin samun nasara a wasaninta guda bakwai da ya rage mata lallai zata kafa tarihin daga kofin firimiya lig na Ingila cikin shekaru 24.
Shin kuna ga zata kai ga Nasara cin Kofin ?


