Kocin Bassey Ya Yi Murabus Daga Ranchers Bees,
Babban Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Ranchers Bees, Kaduna, Patrick Bassey ya yi murabus nan take, in da bayyana damuwarsa game da matsalolin tsaro, rashin kyawun yanayin walwala da kuma ci gaba da tsoma baki a harkokin horaswa daga shugabannin kungiyar.
A cikin wata takardar ya rubuta mai dauke da kwanan wata 2 ga Disamba 2025 kuma aka aika wa Shugaban kungiyar, kocin ya nuna godiyarsa na bashi damar yin aiki, yana mai cewa matsayin kungiyar a yanzu – na biyu a teburin gasar NNL, bayan wasanni uku – shaida ce ta ci gaban da aka samu a karkashin jagorancinsa.
Duk da haka, ya jaddada cewa yanayin aiki ya zama “mara kyau kuma ba zai iya jurewa ba,” yana barazana ga tsaronsa da kuma burin ci gaba da kungiyar.
Damuwa Kan Tsaro: “Wani Abu Mai Hadari Kuma Mara Kyau”
Kocin ya bayyana “rashin kulawa ga al’amuran tsaro,” yana ambaton umarnin da aka ba wa ƙungiyar na fara tafiye-tafiyen dare bayan wasannin waje da kuma daga sabon filin wasansu da ke Minna, Jihar Neja – wani abu da ya kira rashin aminci kuma ba za a iya yarda da shi ba.
Ya ƙara da zargin barazanar da wasu magoya baya ke yi wa rayuwarsa kafin da kuma bayan wasanni, ya ƙara da cewa hukumar, a lokuta daban-daban, “ta sa magoya baya su ci zarafin sa.
Rashin Jin Daɗi da Yanayin Aiki
Wasikar murabus ɗin ta kuma nuna gazawar ƙungiyar na samar da kayan jin daɗi na musamman ga ‘yan wasa da jami’ai.
A cewarsa, a kwai rashin sansanin da kuma sanya Ido kan ‘yan wasa ya yi wahala, yayin da rashin kayan wasan da ake buƙata, gami da takalman ƙwallon ƙafa, ke kawo durkushewar aikin, ga kuma batun ciyar da ‘yan wasa abin da ba a saba gani ba,” ya bayyana cewa sau da yawa ana tilasta wa ƙungiyar ta dogara da abincin da aka riga aka shirya da shugabanni ke bayarwa yayin da suke shirin wasannin lig.
A wani lokaci, ya lura da nuna wariya a lokacin wasan lig a Kebbi, inda aka bai wa ‘yan wasa ₦10,000 kowannensu don ciyar da su yayin da shi kuma ake bashi ₦5,000 kacal.
Kocin ya yi Allah wadai da yadda ake daidaita biyan kuɗin bonus ɗinsa da na ‘yan wasa, yana mai kiransa rashin ƙwarewa.
Shisshigi a bangaren Horaswa “Abin da ke Shafar Ci gaban Ƙungiya”
Wani babban batu da aka ambata shi ne katsalandan da shugabannin ƙungiyar ke yi a cikin shawarwarin bangaren horaswa.
Kocin ya ce ana masa katsalandan lokacin da ya shiga daki da yan wasa saboda jami’ai galibi suna shiga yayin tattaunawar ƙungiya har ma suna sanya baki kan ‘yan wasa da za’a can lokacin wasanni.
“Ba zai yiwu a Ci gaba ba”
Kocin ya kammala da cewa yanayin aiki mai ban tsoro, tare da gazawar gudanarwa da ke ci gaba, ya sa ba zai yiwu ya ci gaba da aikinsa ba.
Ana sa ran murabus dinsa zai haifar da tattaunawa mai zurfi a tsakanin al’ummar kwallon kafa ta Kaduna, musamman ganin yadda Ranchers Bees suka fara kakar wasa mai kyau.
Har yanzu kungiyar ba ta fitar da wani martani a hukumance game da wannan kamari ba.


