Wata kotu a kasar Faransa ta sami wani tsohon madugun ‘yan tawaye a kasar Kwango, a lokacin yakin kasar na biyu, Roger Lumbala, da laifin hada baki wajen cin zarafin Bil’adama, ta yanke masa hukuncin daurin shekau 30 a gidan fursina, kamar yadda wani jami’in kasar yayi bayani.
Kungiyoyin kasa da kasa masu rajin kare tafarkin shari’a, sun yabawa wannan hukuncin, suna cewa matakin yayi dai dai wajen ganin wadanda suke da hanu a rikicin da ya halaka miliyoyin rayuka sun fuskanci shari’a.
Amma masu gabatar da kara sun so da kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Zarginda aka sami Lumbala da laifi, sun wakana a wani matakin soja da aka yi tsakanin shekara ta 2002-2003 a arewa maso gabashin jamhuriyar demokuradiyyar kwango, karkashin wata kunigyar ‘yan tawayen Kwango wacce Uganda ta marawa baya.


