Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da nadin mutum uku da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata domin zama jakadun Najeriya a ƙasashen waje.
Waɗanda aka tabbatar sun haɗa da:
Aminu Muhammad Dalhatu daga Jihar Jigawa da Lateef Kayode Kolawole Are daga Jihar Ogun sai kuma Emmanuel Ayodele Oke, CFR daga Jihar Oyo.
Majalisar ta tabbatar da nadin nasu ne bayan nazarin rahoton kwamitin harkokin waje na majalisar, wanda ya gudanar da tantance su a makon da ya gabata.
Shugaba Tinubu ya tura sunayen jakadun uku ne tun ranar 26 ga Nuwamba, a matsayin rukuni na farko tun bayan zamansa shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Sai dai har yanzu akwai wasu mutum 64 da aka aike sunayensu domin nadin jakadanci, amma majalisar ba ta kammala tabbatar da su ba.


