Kasashen Mali da Burkina Faso sunce za su hana Amurkawa izinin shiga kasashen su, martani kan irin wannnan matakai da gwamnatin Trump ta bada sanarwa akai a farkon watan Disemban 2025.
A cikin sanarwar da ma’aikatun harkokin kasashen wajen biyu suka bayar daban-daban a daren litinin, kasashen biyu da suke Afirka ta yamma sunce suna daukar wannan matakine a zaman “martani” bayanda fadar White House ta bada sanarwar ranar 16 ga watan disemba cewa shugaban Amurka Donald Trump, zai kara kasashen su da wasu biyar a jerin kasashen da Amurka zata iya haramtawa shiga kasar.
Fadar White House tace jerin kasashen da matakin zai shafa zai fara aiki daga 1 ga watan Janairu na sabuwar shekara, ya shafi kasashe da suka ci gaba nuna rashin tantan-cewa na kwarai, yin kididdiga, da kuma musayar bayanai domin kare Amurka ta fuskar tsaro da kuma barazana kan zaman lafiya.
Mali ta fada a talata cewa shawarar da hukumomi a Washington suka dauka na sanya kasar cikin jerin kasashen da zata haramtawa shiga, ta yi hakan ne ba taredaa wata tuntuba ba, kuma hujjar data bayar na yin haka yayi karo da hakikanin al’amura.
Kasashen Mali da Burkina Faso ba sune kasashe na farko da suka dauki irin wannan mataki da ya shafi Amurkawa ba, bayan gwamnatin Trump ta auna su da irin wannan mataki.
Ranar 25 ga watan Disemba da ta wuce kasar Nijar makwabciyar wadannan kasashe ta bada sanarwar cewa zata daina bada Visa ga Amurkawa, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka fada, daga bakin masana harkokin difilomasiyyar kasar.
A cikin watan Yuni ne kasar Chadi ta bada sanarwar dakatar da bada visa ga Amurkawa, bayan da gwamnatin Amurkan ta saka kasar a jerin kasashe 12 da haramcinta shafa.


