Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Masoya Kungiyar Kwallon Kafar Morocco Suna Cikin Farin Ciki Bisa Hukuncin Kotu
Published: March 19, 2026 at 8:54 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Masoya kungiyar kwallan kafa ta kasar Morocco sun nuna farin ciki bisa hukuncin da kotu ta yanke na baiwa kungiyar nasarar cin gasan kwallon kofi na nahiyar Afirka da ci 3-0 kan kasar Senegal. Amma wasu sun ce a bi abun a sannu, yayin da Senegal ke shirin daukaka kara don kalubalantar hukuncin da ya girgiza harkar kwallon kafa a nahiyar afirka.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka wato (CAF) ta ayyana kasar Morocco a matsayin wadda ta lashe gasar, bayan da tayi hukuncin cewa ‘yan wasan Senegal sun rasa damar su bayan da suka fice daga fili na tsawon mintuna 14 don nuna adawa da penalty da aka bawa daya bangaren.

Duk da Senegal ta dawo daga baya ta kuma ci kwallo daya a karin lokaci da aka bayar, yayin da Morocco bata ci komai ba, CAF ta sauya sakamakon, inda ta bawa Morocco ci 3, ita kuma Senegal ba ko daya.

Hukumar kwallon kafa ta Senegal tace zata daukaka kara kan wannan hukunci da ba’a taba ganin irin sa ba, kuma baza’a yadda dashi ba. Ita kuma kungiyar kwallon kafa ta Morocco tace daukan tsauraran matakai zai taimakawa kwallon kafa a Afirka.

Afrika, Labarai, Wasanni

Post navigation

Previous Post: Trump: Isra’ila Ta Daina Kai Hari Ga Duk Cibiyar Iskar Gas
Next Post: Gwamnatin Kasar Ghana Ta Rage Farashin Cocoa

Karin Labarai Masu Alaka

Kasashen Yankin Gulf Sun Bada Sanarwa Afrika
Najeriya Zata Kara Mai Da Take Hakowa Afrika
Dogarawan Ruwa Na Amurka Suna Yunkurin Shiga Wani jirgin Dakon Mai Da Aka Allakan Ta Da Venezuela Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu Zai Ziyarci Jihohin Borno,Bauchi Da Legas Labarai
Bisa Alamu Hadinkan Kasashen Yankin Sahel Zai Haifar Da Nagarta Afrika
An Zargi Kasar Eritrea Da Cin Zarafin Sojojin Habasha Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hafsan Sojin Najeriya: Samar Da Sabbin Wajen Horas Da Sojoji Zai Inganta Tsaro Tsaro
  • Kungiyar ‘Yan Ta’adda Masu Alaka Da ISIS Sun Kashe Mutane A Congo Tsaro
  • An Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Somaliya Labarai
  • Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
  • Jami’an Tsaro Na Amfani Da Damar Su Wajen Cin Zarafin Jama’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Afirka Ta Kudu Ta Tsare Wasu Amurkawa Amurka
  • Za A Rantsar Da Mainasara Kogo A Matsayin Shugaban Kundin Da’ar Ma’aikata Labarai
  • Ukraine Ta Mika Wa Amurka Daftarin Yarjejeniya Da Rasha Sauran Duniya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.