Matatar mai ta Dangote a Najeriya ta fitar da takardun kwangila don sayar da man gas da man jirgin sama, a cewar wani dan kasuwa.

Dangote yace Zai saki gangar mai na jiragen sama tan 44,000 don a yi lodin shi ranar 20 zuwa 22 ga wannan Watan sannan kuma zai saki a kalla gangar man gas 40,000, wanda shi kuma za’a fara lodin sa ranar 15 har zuwa 30 ga Watan Maris.
Matatar mai ta Dangote bata ce komai game da tambayoyin da aka yi mata kan lamarin ba.


