Jajircewa da muka nuna a baya ita ta sa Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya sake dauko ni don na ja ragamar ma’aikatar tsaro ta kasa. Tsarin aikin mu shine, ba nuna banbanci na addini ko kabilanci, haka kuma ba sani ba sabo wajen gabatar da aiki.
Mu duka ‘yan Najeriya ne sai mun hada hannu da tunanin mu waje daya sannan zamu iya samun zaman lafiya. Babban abun da yasa muke yin nasara shi ne son kasa da kishin ci gabanta.
Zamu hada kan dukannin jami’an tsaro waje daya, don ganin an yi aiki tare da samar da mafita ga kasa. A can baya mun fuskanci kalubale na rashin hadin kai, amma yanzu burin mu shine mu taho da kowa a cikin sabuwar tafiya.
Shugaban kasa ya dau alwashin bamu damar yin aiki ba tare da wata damuwa ba, ya kuma ce zai bamu dukkan wata gudunmawa da muke nema wajen kawo karshen ta’addanci a kasar. Na tabbatar ma sojoji wannan kudurin na aiki tukuru don kawo karshen matsalolin rashin tsaro a kasar.
Babban abun da muke nema shi ne gudunmawar Allah da ta jama’a wajen taya mu da addu’a da bada bayanan siri a duk lokacin da aka ga wani abu da bai yi tsari da zaman takewar al’ummah ba.
Duk wanda yake tare da Allah to zai ga nasara a cikin al’amuransa, don haka zamu yi aiki da kowa a wannan sabon matsayi.
Bamu da wani shiri na yin sulhu da ‘yan ta’adda, don kuwa basu da hujja ta kama talakawa da basu ji basu gani ba, mun dau damarar yakar su haikan, daga nan har illa-masha Allah.
Gwamnatin mu a shirye take taga mun kawo karshen ‘yan ta’adda a kowane hali, don haka muna neman addu’o’in ‘yan Najeriya a kowane hali da neman nasara akan duk bata gari.


