Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana bijirewar cututtuka ga maganguna a matsayin babban al’amari dake kawo cikas da barazana a bangaren kiwon lafiyar jama’ah.
Najeriya dai ta kasance kasa ta 19 wajen rasa rayuka a cikin kasashe 204, kuma ana danganta mutuwar mutum dubu dari biyu da sittin da uku da dari hudu da matsalar Anti Microbial Resistance (AMR).
Dr. Muslim Bello Katagum yace AMR na nufin yadda cututtuka basa jin magani sakamakon shansu da ake yi ba bisa ka’ida ba.
Ganin yadda wannan matsala ke kara ta’azzara a duniya yasa Danida Alumni wato Dalibai da suka samu horo daga Danish International Development Agency, wato hukumar dake kula da cigaban kasashe ta kasar Denmark suka gudanar da taron a Abuja, domin watar da kan masu ruwa da tsaki da suka hada da NAFDAC, Standard Organisation Of Nigeria (SON), manoma, da sauransu domin tattauna hanyoyin wayar da kai don shawo kan matsalar AMR.
Sakataren Danida Alumni Nasiru Usman yace sun lura wannan matsala na daga cikin abubuwan dake damun Najeriya shiya suka shirya taron domin domin gwamnati ta kara maida hankali da sa ido kan lamarin.

Wakili daga Gonar Medogi Idris Usman Ibrahim yace taron ya kara fahimtar dasu yadda abun yake, inda ya kara da cewa a yanzu zasu maida hankali wajen bin ka’idar magani ga dabbobi da shuka.
Khadija Muhammad dake aiki da ma’aikatar kula da muhalli a sashen hana gurbacewar muhalli da kuma kula da lafiyar muhalli, jan hankali tayi wajen kula da tsaftar muhalli don gujewa cututtuka.
Matsalar AMR dai na daga cikin manyan matsaloli da hukumar lafiya ta duniya (WHO) tafi maida hankali akai a yanzu,ganin yadda matsalar ke haifar da salwantar rayuka da yaduwar cututtuka.


