Kamfanin makamashi na Heirs Energies na Najeriya tare da kamfanin mai na kasar NNPC, sun sanya hannu a kan yarjejeniya tare da wasu masu zuba jari su 5 domin tare irin gas da ake konawa ba tare da amfanin komai ba lokacin hakar mai, da nufin maida shi na kudi.
Najeriya tana da gas mafi yawa da aka sani a fadin nahiyar Afirka, kuma tana fatar ganin an yi amfani da shi wajen bunkasa masana’antu tare da rage fitar iska mai gurbata yanayi.
Najeriya na kokarin fadada yin amfani da iskar gas din da ake narkarwa, tare da rage yawan kona shi haka a banza sai dai kuma alkaluma na bankin sun nuna cewa a shekarar da ta shige yawan kona iskar gas a banza ya karu da kashi 12 cikin 100.
Wannan yarjejeniya da aka sanya ma hannu wani bangare ne ta kokarin masu hannu da shuni a harkar mai a Najeriya na bunkasa samar da iskar gas a cikin gida kuma a karkashinsa a kullum za a rika sarrafa murabba’in kafa miliyan 18 na iskar gas a wani yankin tonon mai da kamfanin Heirs Energies ke gudanarwa.
Duk da alkawarin da Najeriya ta yi na kawo karshen yadda ake kona iskar gas a banza da wofi, kasar ta kona iskar gas har ta dala miliyan dubu daya da hamsin, inda ta saki iska mai guba ta CO2 har ton miliyan 16 a bisa wasu alkaluma da gwamnatin kasar ta bayar.


