Mai tsaron ragar ƙungiyar kwallon kafa ta Kamaru Andre Onana ya sake fuskantar wani mummunan rauni hakan yasa aka cire shi daga tawagar Kamaru da za ta fafata a gasar cin kofin kasashen Afirka da ke tafe.
Dan wasan mai shekaru 29 ya sha wahala a kakar wasa ta 2025-26, bayan ya rasa matsayinsa na mai tsaron raga na 1 a Manchester United kafin aka ba shi damar komawa kungiyar Trabzonspor ta Turkiyya a matsayin aro na tsawon kakar wasa a watan Satumba.
Ba a saka Onana a cikin jerin ‘yan wasa masu tsaron raga hudu ba duk da cewa Kamaru ta zabi ‘yan wasa hudu.
An yi ta jan ido a ranar Litinin lokacin da Kamaru ta fitar da ‘yan wasa 28 da za su fafata a AFCON, wanda za a fara a ranar Lahadi, 21 ga Disamba in da Morocco mai masaukin baki za ta fafata da Comoros.
Duk da zabar masu tsaron gida hudu, Onana bai shiga cikin jerin ‘yan wasan Indomitable Lions ba.
‘Yan wasa biyu da aka sanya a cikin tawagar sune dan wasan gaba na United Bryan Mbeumo da dan wasan tsakiya na Brighton & Hove Albion Carlos Baleba, wanda aka alakanta da komawa Old Trafford a lokacin bazara.
Tsohon ɗan wasan gefe na Tottenham Hotspur Georges-Kevin Nkoudou – wanda yanzu yake bugawa ƙungiyar Diriyah Club ta Saudiyya wasa – shi ma ƙasarsa ta zaɓe shi.
A hukumance: Tawagar ‘yan wasa 28 na Kamaru wadanda ba su hada da Onana ba
Tawagar Kamaru ta 2025 AFCON:
Masu tsaron gida: Devis Epassy, Simon Omossola, Simon Ngapandouetnbu, Edouard Sombang
Masu tsaron baya: Samuel Junior Kotto, Gerzino Nyamsi, Jean-Charles Castelletto, Nouhou Tolo, Flavien Enzo Boyomo, Nagida Mahamadou, Junior Tchamadeu, Christopher Wooh, Darlin Yongwa
‘Yan wasan tsakiya: Martin Ndzie, Carlos Baleba, Arthur Avom, Eric Junior Dina Ebimbe, Fidel Brice Ambina, Danny Namaso, Christian Bassogog, Georges-Kevin Nkoudou, Jean Junior Onana, Olivier Kemen
Masu wasan gaba: Bryan Mbeumo, Christian Kofane, Frank Magri, Karl Etta Eyong, Patrick Soko.
Hukumar Kwallon Kafa ta Kamaru ta kori kocin da ya lashe gasar AFCON sau biyar a rana ɗaya.

Hukumar Kwallon Kafa ta Kamaru – karkashin jagorancin tsohon dan wasan Barcelona, Chelsea da Inter Milan Samuel Eto’o – ta salami mai horaswa Marc Brys a ranar da aka sanar da sunayen ‘yan wasan da zasu fafata mata a gasar cin kofin kasashen Afirka AFCOB
Inda suka nada David Pagou a matsayin wanda zai maye gurbin Brys, kasar Kamaru za su fafata da Gabon a wasan farko cikin makonni uku kacal (24 ga Disamba). Kamaru kuma za ta fafata da Ivory Coast (28 ga Disamba) da Mozambique (31 ga Disamba) a matakin rukuni.


