Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana shirin daukar sabbin ma’aikatan tsaro sama da 94,000 domin ƙarfafa yaki da tashin hankalin a faɗin ƙasar.
A cikin shirin ta, Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda (PSC) tare da Rundunar ’Yan Sanda (NPF) za su dauki ’yan sanda 50,000, inda za’a bude shafin neman aikin daga ranar 15 ga watan Disamba 2025, zuwa 25 ga Janairu 2026.
A wata sanarwa daga Hukumar, an bayyana cewa daukar aikin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na ƙarfafa tsaron cikin gida da faɗaɗa ƙarfin ’yan sanda.
Ana bukatar masu neman aikin su mallaki takardar shaidar kammala karatun Sakandare ta SSCE/NECO ko makamantan su da ke da a ƙalla Credits biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.
Wani jami’in soji wanda bashi da izinin magana na manema labarai yace، Rundunar Sojin kasa ta Najeriya na iya daukar sojoji 14,000. Majiyoyi kuma sun tabbatar da cewa Rundunar Sojin Ruwa da Ta Sama za su ƙara yawan ma’aikata.
A baya, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta sanar da daukar ma’aikata 30,000 a hukumomin tsaron da ba na Soja ba (paramilitary).
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan tsaro a ranar 26 ga Nuwamba, 2025, tare da umarnin daukar ƙarin ma’aikata a hukumomin tsaron kasar.


