Takaddamar Gwamnoni da NNPC yayinda, hankali ya tashi kan zargin gibin kudaden mai Dala Biliyan $42.
Sabon rikici ya kunno kai a tsakanin NNPC Limited da Kamfanin da ke yi wa Kungiyar Gwamnonin Najeriya aiki (Periscope Consulting), kan zargin cewa an kasa tura kudaden mai na dala biliyan $42.37bn zuwa Asusun tarayya tsakanin 2011 da 2017.
Rahoton bayan taron Kwamitin rabon arzikin kasa FAAC na Nuwamba 2025, ya nuna cewa NNPCL ta ƙi amincewa da sakamakon binciken Periscope, tana mai cewa ta tura dukkan kudaden da ake zargi, amma Periscope ta dage cewa akwai gibi mai yawa a rahotannin NNPC.
Sabani tsakanin ɓangarorin biyu ya sa FAAC ta umarci su shiga zaman sulhu domin daidaita bayanai sai kuma binciken dai ya fito ne daga korafe korafen gwamnoni kan rashin bayyananniyar hanyar tura kudaden mai, wanda ya haifar da dakatar da taron FAAC a baya.
Har yanzu ana ci gaba da aikin daidaitawa, yayin da rikicin ke jefa damuwa kan kudaden shiga da jihohi ke dogaro da su.


