Rundunan ‘Yan Sanda ta miƙa Miyagun Ƙwayoyi na kuɗi sama da Naira Miliyan 12 wa NDLEA.
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar ta mika Miyagun Ƙwayoyin da ta kama a shogon wani mai suna Ogbu Simon a garin Ningi wa Hukumar Hana sha da fataucin Miyagun Ƙwayoyin NDLEA.

Da yake Miƙa miyagun kwayoyi wa hukumar Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Bauchi CP Sani Omolori ya ce Miyagun Ƙwayoyin nauyinsu ya kai kilogiram 161, ƙiyashin kuɗin su ya kai Naira miliyan 12 da dubu ɗari biyu.

Wadda ake zargi da Safarar kwayoyin Ogbu Simon ya kawo kwayoyin ne daga Onisha na Jihar Anambra. Kuma Jami’an yan’sanda sun samu bayanan sirri a lokacin da ake shigar da buhu hunan ƙwayoyin cikin Shagon sa dake Ningi.

Kwamishinan ‘yan sanda ya bada tabbacin ci gaba da jajircewar Rundunar wajen yaƙi da ta’ammalin miyagun ƙwayoyi da kuma aikata laifuffuka.

ƙwayoyin da ta kama sun haɗa da sachet 17,500 na Tramadol da fakiti 487 na Diazepam (D5)—ga hukumar NDLEA ta jihar Bauchi domin ci gaba da bincike.


