Magajin garin New York, Zohran Mamdani ya kare shawarar da ya yanke na soke wasu dokoki da magabacin sa Eric Adams ya zantar, bayan da aka kama shi Adams din da karban haramtattun kudaden da aka tara don zabe.
A cikin dokokin da yawa da ya zartar ya hada da barin jami’an tsaro na kasa, ciki har da jami’an shige da fice da su yi amfani da wani ofishi dake Rikers Island, inda nan ne babban gidan kaso na birnin, wadda tuni wannan dokar wata kotu ta soke ta.
Sabon magajin garin ya soke dokokin da Adams ya zartar, wanda ya ce zasu Magance nuna kiyayya ga yahudu, Mamdani, musulmi, wanda wasu ke zargin yana da ra’ayin kin yahudu, ya shaidawa manema labarai ranar Jumu’a cewa zai yi dokoki da zasu magance nuna kiyayya ga kowane jinsi, kuma zai bawa bada kariya ga yahudawa muhimmanci.


