Sakataren gwamnatin Amurka, Marco Rubio, ranar Jumu’a, yace burin fadar Washington kan Sudan a yanzu shi ne mayar da makaman yaki, har zuwa cikin sabuwar shekara, don barin kungiyoyin agaji su kai taimako.
Yayin da yake jawabi ga ‘yan jarida a wani taro da Manema labarai, Rubio ya ce kasashe suna bawa bangarori makamai, ciki har da aikewa da Makamai musamman ga dakarun sa kai, inda ya kara da cewa fadar Washington na tattaunawa da bangarorin da abun ya shafa.
Ya ce sun tattauna a kan abubuwan da suka dace da duka bangarorin, saboda ba wani bangare da zai iya wani tasiri ba tare da goyon bayan daya bangaren ba, shi yasa muke tattaunawa da duka bangarorin da ke da ruwa da tsaki a wannan abu.
Hukumomin Amurka sun ce sojojin kasar sun kai hare hare da jiragen sama kan sansanin kungiyar ‘yan ta’adda na ISIS da dama a Syria ranar Jumu’a, a wani martani da aka yi kan Jami’an Amurka.
Shugaba Donald Trump ya dau alwashin mai da martani bayan da wani da ake zargin dan ISIS ne ya kaiwa jami’an Amurka hari a karshen makon da ya gabata a Syria.
Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth, ya tabbatar da hare-haren sun fada ne kan mayakan ISIS, kayayyakin su, da makaman su, Kuma ya ce taken harin shi ne OPERATION HAWKEYE STRIKE.
Ya kara da cewa, wannan ba mafarin yaki ba ne, ramuwar gayya ce, yau mun farauto, kuma mun kashe makiyan mu.


