Sanyi mai tsanani ya kase wasu bakin haure ‘yan Afirka a kusa da bakin iyakar Morocco da Aljeriya.
Kungiyoyin kare hakkin bil Adama a kasar dake Afirka ta Arewa sun bayyana wannan a matsayin babban abin damuwa kuma abinda ya keta ‘yancin zirga-zirgar murtane.
Wata gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil Adama a kasar Morocco, ta ce an gano gawarwakin maza 7 da mata biyu a yankin Ras Afour mai tsaunuka, inda sanyin hunturu yake yayi tsanani sosai.
Kungiyar ta ce wadannan bakin haure ‘yan gudun hijira sun mutu a sanadiyyar sanyi mai tsanani wanda jikinsu dake gajiye ba zai iya dauka ba.
An ce daya daga cikin ‘yan gudun hijirar dan kasar Guinea ne.
A duk shekara, dubban ‘yan Afirka dake kwadayin zuwa kasashen turai su na bi ta cikin hamadar Sahara zuwa kasashen Afirka ta yamma daga inda suke fatan tsallakawa zuwa turai, amma irin wannan balaguro yana da tsananin hadari, kuma daruruwa suna mutuwa ba tare da sun kai inda suke son zuwa ba.


