Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa hukumomin tsaro bisa kokarinsu na kubutar da dalibai 100 na makarantar Papiri Catholic School da ke Jihar Neja.
Yayin da ya bayyana farin cikinsa kan dawowar daliban cikin lafiya, Shugaba Tinubu ya kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar da gaggawar kubutar da sauran dalibai 115 da malamansu da ke hannun masu garkuwa.
Shugaban Kasar ya tabbatar wa iyayen daliban cewa gwamnatin tarayya tare da gwamnatin Jihar Neja na aiki tare domin ganin an dawo da dukkan wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
“Ina da cikakken bayani kan dawowar dalibai 100 na makarantar Catholic da ke Jihar Neja.
Ina murnar wannan cigaba tare da Gwamna Umar Bago, kuma ina yabawa hukumomin tsaro bisa jajircewarsu tun bayan mummunan lamarin da ya faru ranar 21 ga Nuwamba.
“Umarni na ga hukumomin tsaro a bayyane yake, dole ne a ceto dukkan daliban da sauran ’yan Najeriya da aka sace, a dawo da su gida lafiya sannan dole mu tabbatar da an ciro kowa ba tare da barin kowa a baya ba.
Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tare da jihar Neja da sauran jihohi domin kara tsaro a makarantun mu da samar da mafi ingancin muhalli na ilmantarwa ga yaranmu.
“Daga yanzu, hukumomin tsaro tare da haɗin gwiwar gwamnoni dole su dakile sake faruwar irin wadannan sace sacen, ya kuma zama wajibi yaranmu su daina zama a wajajen da ’yan ta’adda za su rika kai hari don karya karatunsu da jefa kan su da iyalansu cikin bakin ciki,” in ji Shugaba Tinubu.


