Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da sauya sunan Federal University of Medical Sciences, Azare zuwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi University of Medical Sciences, Azare, domin girmama marigayi fitaccen malami kuma dattijo a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Sanarwar sauya sunan jami’ar ta zo ne a matsayin girmamawa ga irin rawar da marigayin ya taka wajen yaɗa ilimin addini, tarbiyya da zaman lafiya a Najeriya da ma ƙasashen waje.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shahara wajen koyar da ilimi, da’awa da kuma tsayawa kan gaskiya da hadin kan al’umma.
A cewar Shugaban Ƙasa, wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na karrama manyan ’yan Najeriya da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimar al’umma da ci gaban ƙasa, musamman a fannonin ilimi da tarbiyya.
Shugaba Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin wani ginshiƙi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin kira ga Allah tare da koyar da addini.
Ya yi fatan zuri’arsa za su cigaba da ɗabbaƙa ayyukan alheri da babban malamin ya aiwatar a lokacin da yake raye.


