Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga Afrika
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugaba Trump Ya Amince Da Tsawaita Cinikayya Tsakanin Amurka Da Kasashen Afirka
Published: February 6, 2026 at 10:43 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar talatar makon nan ne shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hanu na kara wa’adin cinikayya tsakanin Amurka da kasashen Afirka ba tare da haraji ba da ake kira AGOA, na tsawon shekara daya, zuwa 31 ga watan Disamba shekara ta 2026.

Kara tsawon wa’adin ya kawo karshen zaman zullumi game da makomar shirin, yayinda kasashen duniya suke ji da matsanancin haraji da shugaban na Amurka ya azawa kasashen duniya ranar 2 ga watan Afrilun bara. Karewar wa’adin cinikayyar da ake kira AGOA ya jefa dubban ayyuka a nahiyar Afirka cikin hadari.

Kasar Lesotho, kasar Afirka da ta fi ko wacce dogaro kan kayayyaki da take sayarwa a kasuwannin Amurka, tsawaita wa’adin, ya sassauta zaman zullumi, ko da shike rashin tabbas din har yanzu yana nan.

“Ina da kwarin guiwar za’a sami wani abu na lokaci mai tsawo,” inji ministan harkokin kasuwanci na Lesotho Mokheti Shelile a hirar da yayi da kamfanin dillancin labarai na Reuters ofishinsa. Ya kara da cewa karin wa’adin na shekara daya bai dace da yanayin harkokin cinikayyar kasarsa ba. Bangaren sake-sake shine kan gaba na kayayyaki da Lesotho take sayarwa a kasashen ketare.

A watan Afrilun bara Amurka ta dorawa Lesotho harajin kashi 50 cikin dari, daga bisani gwamnatin Trump ta rage shi zuwa kashi 15 cikin dari, duk da haka wannan harajin yana da nauyi ga Lesotho wacce ta dogara kan cinikin kayayyakin sawa da Amurkawa suke saye.

Afrika, Amurka, Labarai

Post navigation

Previous Post: Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Matsalar Tsaro A Shiyar
Next Post: Kasar Morocco Ta Kwashe ‘Yan Kasar Daga Sassan Ambaliyar Ruwa

Karin Labarai Masu Alaka

Sojojin Kasar Isra’ila Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Hamas Labarai
Shugaban Amurka Donald Trump Ya Nanata Aniyar Mallakar Greeland Daga Kasar Denmark Amurka
Shugaba Donald Trump Yabada Umarnin Hana Jiragen Dakon Mai Shiga Venezuela Amurka
Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan Labarai
Shugaba Tinubu Ya Turawa Majalisa Sunayen Mutane Biyun Da Zasu Shugabanci Sashin Albarkatun Mai Labarai
Hukumar DSS Ta Sake Kama Abubakar Malami Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Dalibin Jami’a Ya Rasa Ransa A Birnin Dakar Yayin Zanga Zanga
  • Kasar Zimbabwe Ta Samar Da Dokar Tsawaita Mulkin Mnangagwa Zuwa 2030
  • ‘Yan Bindiga Sun Karya Alkawarin Dakatar Da Kai Hare Hare A Najeriya
  • Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo
  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Farashin Zinari Yayi Tashin Gwauron Zabi Amurka
  • Hukumar CAC Zata Dakatar da POS Mara Rijista a Kasar Najeriya
  • Kamfanin Bitcoin A Korea Ta Kudu Yayi Kuskuren Turawa Masu Mu’amala Da Kamfanin Kudade Afrika
  • Gwamnatin Amurka Tana Ganawa Da Manyan Jami’an Leken Asiri Amurka
  • Shirin: Lafiya Jari Ce 11.21.25 Kiwon Lafiya
  • Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Namibiya Tayi Watsi Da Yarjejeniya Tsakanin Ta Da Kamfanin Total Labarai
  • Akwai Bukatar Bin Dokokin Tuki A Kan Hanyoyi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.