Farfesa Wole Soyinka ya yi gargaɗi ga Shugaba Bola Tinubu kan yadda ake gudanar da tsaro da kuma amfani da jami’an gwamnati wajen kare wasu ‘yan tsiraru masu kusanci da fada.
Yayin bikin bayar da kyaututtuka na Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism a Legas, a wani bidiyo da ya yadu, Soyinka ya ce ya yi mamakin ganin “babbar rundunar tsaro” da aka bai wa Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa, a Ikoyi.
Ya bayyana cewa yawan jami’an tsaron da ya gani “ya isa ya mamaye ƙaramar ƙasa,” lamarin da ya sa ya tuntubi mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, domin neman bayani.
Soyinka ya ce bai dace ‘ya’yan shugabanni su gaji karfin gwamnati ko su yi yawo da tsaro fiye da kima ba, yayin da ƙasar ke fama da hare-hare, garkuwa da mutane da rashin tsaro a sassa da dama.
Ya ƙara da cewa irin wadannan albarkatun tsaro ya fi dacewa a tura su wuraren da ake bukata, ba wajen kare masu gata ba.


