Kasar Saudiyya ta kere kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Oman, Kuwait da sauran su wajen yawan ‘yan kasar da ke kai ziyara kasar Bahrain don yawon bude ido a shekarar 2025.
Wannan ya biyo bayan irin kyakkyawar alaka da hanyoyin saukaka zirga- zirga tsakanin kasashen biyu.
Karin yawan ‘yan Saudiyya da ke zuwa Bahrain ya bunkasa sashen yawon bude ido na kasar sannan ‘yan Saudiyya sun zamo jagaba wajen kai ziyara Bahrain don ganewa kan su al’adu, more rayuwa da kuma samun nishadi.
Tattalin arzikin Bahrain ya samu kyakkyawan sauyi, inda aka samu ci gaba a fannin kula da baki, kasuwanci da kuma zirga-zirga, a yayin da ake tsammanin samun baki daga Saudiyya fiye da miliyan 9.7 a shekarar 2025.
Duk da cewa Bahrain kasa ce dake da farin jini wajen masu yawon bude ido, amma gudummawar da Saudiyya ke bawa sahen bude ido na kasar ya zarce na kasashe kamar Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Oman da Kuwait, abin da ya kawu sauyi na bunkasa tattalin arzikin Bahrain ta fannin yawon bude ido.


